Isa ga babban shafi
Jordan

Obama ya yi Allah wadai da kisan da IS ta yiwa dan kasar Jordan

Shugaban Kasar Amurika, Barrack Obama, ya yi Allah wadai da kisan da kungiyar IS mai ikirarin kafa daular Islama ta yi wa Maaz al-Kassasbeh, matukin jirgin sama dan Asalin kasar Jordan

Shugaban Amurka, Barack Obama.
Shugaban Amurka, Barack Obama. REUTERS/Mandel Ngan/Pool
Talla

A cewar Obama, matukar wannnan hotan bidiyon  gaske ne, to lallai wannan na nunin  yadda kungiyar ta kai matuka a rashin tausayi da jahilci.

A hotan bidiyon, kungiyar ta nuna kisan da ta yiwa Mazz al-Kassasbeh  mai shekaru 26 ta hanyar kona shi da ransa a wani keji na karfe.

Gidan talabijin na kasar Jordan ya tabbatar da mutuwar Kassasbeh, sai dai ya bayyana cewa, tun a ranar 3 ga watan jiya Kungiyar ta kashe shi.

A dayan bangaren kuwa, Dakarun Kasar Jordan, sun lashi takobin daukan fansa kisan jami'inita da IS ta yi, yayinda mai magana da yawun Dakarun, Janar Mamduh Al-miri ya bayyana cewa, zasu rama kwatankwacin abinda IS ta yi masu.

Kungiyar ta kama Kassasbeh ne bayan jirgin da ya ke ciki ya fado a watan disamba a hanyarsa ta aiwatar da aikinsa a Arewacin kasar Syria, yayinda kasar ta Jordan na cikin jerin kasashen da suka yi kawance da Amurika domin yakar kungiyar IS.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.