Isa ga babban shafi
Libya

An dakatar da tattaunawar sasanta rikicin Libya

Majalisar Libya da kasashen duniya suka amince da ita ta dakatar da wakilcinta daga zaman tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta tsakanin bangarorin da ke rikici domin samar da zaman lafiya a kasar.

An yi Bikin cika shekaru 4 da kaddamar da zanga-zangar adawa da mulkin Marigayi Kanal Ghaddafi na Libya
An yi Bikin cika shekaru 4 da kaddamar da zanga-zangar adawa da mulkin Marigayi Kanal Ghaddafi na Libya REUTERS/Ismail Zitouny
Talla

Libya dai fada cikin rudani bayan da bangarorin da ke rikici guda biyu ke ikirarin tafiyar da ikon kasar.

Akwai Majalisar gamayyar masu kishin Islama da ke da hedikwata a Tripoli da kuma bangaren Majalisar Tobruk da kasashen duniya suka amince da halaccinta.

Majalisar Dinkin Duniya ta gayyaci bangarorin biyu domin zama teburin sulhu a Morocco a ranar Alhamis, amma kafin lokacin bangare guda ya bayyana ficewa daga tattaunawar.

Babu cikakken bayani akan dalilin ficewa daga tattaunawar daga bangaren Majalisar mai samun goyon bayan kasashen duniya, amma wannan na zuwa ne bayan wani mummunan hari da aka kai a Al Qoba inda mutane kusan 40 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.