Isa ga babban shafi
Ebola

Kasashen da ke fama da Ebola sun nemi agaji

Shugabannin kasashen Afrika ta yamma guda uku ma su fama da cutar Ebola sun nemi karin tallafin kudi domin magance cutar baki daya tare da farfado da tattalin arzikinsu a taron Ebola da aka gudanar a birnin Brussels.

Zauren taron Ebola à Bruxelles
Zauren taron Ebola à Bruxelles REUTERS/Yves Herman
Talla

Shugabar Liberia Ellen Johnson Sirleaf da shugaban Saliyo Ernest Bai Koroma da Alpha Conde na Guinea sun yi kira ga kasashen duniya su taimaka da tallafin domin su tayar da komadar tattalin arzikinsu tare da magance cutar Ebola baki daya a kasashen.

Taron ya ba shugabanin kasashen Liberia da Saliyo da Guinea damar ganawa da manyan shugabanin kasashen duniya domin neman gudumawar shawo kan matsalar Ebola da ke yin kisa cikin hanzari.

Sama da mutane 9,700 suka mutu sakamakon Ebola a kasashen yammacin Afrika, yayin da kusan dubu Ashirin da Hudu suka kamu da cutar.

Liberia da Saliyo da Guinea inda cutar ta fi shafa sun ce a yanzu farfado da tattalin arzikinsu ne kawai zai sa a magance cutar Ebola baki daya, kamar yadda shugaba Sirleaf ta shaidawa taron.

Bankin duniya ya kiyasta cewa kasashen guda uku masu fama da Ebola sun yi hasarar kusan kashi 12 na ma’unin kayyakin da ake samarwa a kasashen.

A ranar Litinin asusun lamuni na duniya ya amince ya ba kasar Saliyo bashi da tallafin kudi da suka kai Dala Miliyan 187.

Taron na Brussels ya kunshi wakilai daga kasashe kusan 60 da suka hada da Tarayyar Turai da China da Amurka da kuma Majalisar Dinkin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.