MDD tace akwai sahihanci a zaben Togo
Majalisar dinkin duniya tace Zaben shugabancin kasar Togo da aka ce shugaban kasar mai barin gado Faure Yasumbe ne ya lashe shi da gagarumin rinjaye, wanda yan adawa suka sa kafa suka yi fatali da sahihancinsa ya gudana a cikin haske da walwala.
Wallafawa ranar:
Manzon babban sakataren MDD, a yankin yammacin Afrika Mohammed Ibn Chambas, a birnin Lome babban birnin kasar ta Togo ya bayyana cewa, zaben ya gudana kamar yadda ake bukata
Sai dai shugaban yan adawa Jean Pierre Fabre ya bayyana tabka magudi a zaben, da ya gagara gabatar da shaidun da ke tabbatar da magudin kawo yanzu
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu