Ana ci gaba da samun karuwar masu kamuwa da cutar Ebola a Saliyo da Guinee
Hukumar Lafiyata Majalisar Dinkin Duniya tace an samu karuwar masu kamuwa da cutar Ebola a kasashen Guinea da Saliyo a cikin makwanni biyu da suka gabata.
Wallafawa ranar:
Hukumar tace daga ranar 7 ga wannan wata na Yuni da muke ciki an samu mutane 16 da suka kamu da cutar a yayin da wasu 15 suka kamu a kasar Saliyo.
Cutar Ebola dai ta yi sanadiyar mutuwar mutane 11,158 daga cikin mutane 27,237 da suka kamu da ita a kasashen dake yankin yammacin Afrika.
Duk da cewa yawan masu rasa rayukansu sakamakon kamuwa da ita wannan mummunar cuta ya rago a kasashen Guine Laberiya da Saliyo, har yanzu barazanar na nan bata gushe ba, ganin yadda cutar mai kisa ke da saurin yaduwa tsakanin bani Adam.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu