Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

'Yan Gudun Hijira 14,000 daga Sudan ta Kudu Sun Shiga Sudan

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ‘yan kasar Sudan ta Kudu akalla dubu 14 suka shiga kasar Sudan cikin makonni biyu da suka gabata sakamakon kazamin tashin hankali da ake yi a yankin kasar su.

Kanana yara a Sudan ta kudu
Kanana yara a Sudan ta kudu rfi
Talla

Ann Encontre dake kula da yankin na Hukumar kula da ‘yan gudun hijiyan na cewa akwai mutane sama da dubu 157 da suka tsere daga gidajen su a yankin.

Yawaitan ‘yan gudun hijiran na ciwa Majalisar Dinkin Duniya tuwo a kwarya kasancewar ta na fama da matsalar rashin kudade domin gudanar da ayyukan ta.

Bayanai na nuna kasar Sudan ba ta koransu domin ana kula da muhimman bukatun su kamar harkar lafiya da sauran bukatu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.