Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

'Yan gudun hijira dubu 14 a cikin makonni biyu

Rahotanni daga kasar Sudan ta Kudu na cewa yawan mutanen da suka tsallaka iyaka zuwa makociyar kasar wato Sudan, sun kai dubu 14 a cikin makonni biyu kakcal, sakamakon fadan da ake yi tsakanin ‘yan tawaye da kuma dakarun gwamnati.

Likitocin MSF suna kula da lafiyar Mutanen Sudan ta kudu
Likitocin MSF suna kula da lafiyar Mutanen Sudan ta kudu REUTERS/Andreea Campeanu
Talla

Shugabar ofishin kula da ‘yan gudun hijira ta MDD UNHCR a Sudan ta Kudu Ann Encoutre, ta ce mutanen na cikin mawuyacin hali, sannan ta ce daga cikin kudade dala milyan 150 da suke tsammanin samu a wannan shekara, duka duka abinda ya shiga hannunsu bai wuce kashi 10 cikin dari ba.

An dai share kusan shekaru biyu ana gwabza fada tsakanin ‘yan tawaye magiya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Rieck Machar da kuma dakarun gwmanatin Salva Kiir.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.