Isa ga babban shafi
Kenya-Somaliya

Kenya tace dakarunta zasu ci gaba yakar al-Shebab a Somaliya

Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta, ya sha alwashin barin dakarun sojin Kasarsa a Somaliya domin yakar kungiyar Al-Shebab.Wannan matakin dai, ya saba da shawarwarin da ake baiwa gwamanatin ta Kenya na dawo da dakarunta gida, domin maida hankali kan tunkarar hare haren da ‘yan ta’adda ke kaiwa Kasar. 

Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta
Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta REUTERS/Stringer
Talla

Tun shekara ta 2011 ne gwamanatin kasar ta Kenya ta aika sojojinta Somaliya domin yaki da yan kuniyar Al-Shebab dake da alaka da Kungiyar Al-Qaeda, inda kuma daga bisani sojin suka hada kai da rundunar wanzar da zaman lafiya na Kungiayar Kasashen Afrikaa wannan aikin.
Tuni dai Al-Shebab ta tsaurara ayyukanta na ta’addanci a Kasar Kenya, lamarin da ya saba da makasudin tura dakaru domin samar da tasro kan iyakar kasar ta Kenya.

Kenyatta wanda ya gana da takwarorinsa na kasashen Burundi da Djibouti da Ethpia harma da Uganda, da ke taimakawa wajan tura dakarunsu ga rundunar ta tarrayar Afrika, ya bayyana cewa matsayin Kenya kan wannan batun a bayyana yake.

Shugaban ya kuma jaddada cewa zai cigaba da tabbata kan kudirinsa na maido da zaman lafiya kasarsa tare da daukan mataki kan wadanda ke kokarin hana mutane gudanar da al-amuransu na yau da kullum.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.