Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

'Yan Sanda sun ceto yaran da aka nemi musu kaciya da karfi a Africa ta Kudu

‘Yan sandan kasar Africa ta Kudu sun bayyana cewa sun ceto wasu yara 11, da aka yi yunkurin musu kaciya karfi da yaji. Rahotanni na cewa jami’an tsaron sun kwato yaran ne bayan da iyayensu suka kai rahoton cewa an sace musu ‘ya ‘ya. 

Wasu 'yan kaciya a Africa ta Kudu
Wasu 'yan kaciya a Africa ta Kudu Reuters/Siphiwe Sibeko
Talla

Mai magana da yawun ‘yan sandan yankin Daveyton a gabashin birnin Johannesbourg Daveyton, yace yara 11 masu shekaru 13 zuwa 16 suka ceto daga hannun Masu yin kaciyar, da suka tarkata su daga kan titunan.
Akwai wasu kabilu a nahiyar Africa, dake killace yara a dazuka ko tsaunuka, su shafe lokaci ana horasdasu a matakan zaman magidanta, abinda ya hada da shayi, da kuma darussa kan karfin hali da tarbiya.
Wata hukumar gwamnatin a kasar Africa ta Kudu tace, kusan yara 500 ne suka mutu sakamakon irin wannan al’adar, tsakanin shekaru 2008 da 2014.
Sai dai a duk shekara, akwai yara da matasan da tsautsayi ke fada musu, inda ake guntule musu mazakunta, a lokacin irin wannan al’adar.
A watan Disamban bara aka yiwa wani dan Afrtica ta Kudu mai shekaru 21 dashen azzakari na farko a duniya, bayan da aka guntile mishi nashi a lokaci shayi, kuma yanzu haka budurwar shi ta dauki ciki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.