Isa ga babban shafi
Rwanda-Spain

Birtaniya ta Cafke shugaban hukumar leken asirin kasar Rwanda

Kamun da ‘yan sandar filin sauka da tashin jiragen saman Heathrow na birnin London na kasar Britaniya su ka yi wa shugaban hukumar leken asirin kasar Rwanda Janar Emmanuel Karenzi Karake, dake kan sammacin kungiyar tarayyar Turai ya haifar kakkausar suka daga gwamnatin Kigali

Shugaban hukumar leken asirin  Rwanda, Emmnuel Karenzi Karake.
Shugaban hukumar leken asirin Rwanda, Emmnuel Karenzi Karake. AFP PHOTO/MONUC
Talla

Shi dai Janar Emmanuel Karenzi Karake, dan shekaru 54 a duniya a ranar assabar da ta gabata ne ‘yan sandan Interpol na kasar Britaniya suka kama shi da misalin karfe 9h45 na safiyar ranar assabar da ta gabata a filin sauka da tashin jiragen saman Heathrow dake birnin London, kamar yadda kakakin hukumar yan sanda ta Scotland Yard ya sanar.

Ya kuma kara da cewa, an kama shi ne karkashin sammacin da Kungiyar Tarayyar Turai, ta hannun mahukumtan kasar Spain ta gabatar ne, dangane da zarginsa da aikata laifukan yaki kan fararen hula a kasar Rwanda.

 

Sai dai kuma wata majiyar shara’a daga birnin Madrid na Spain ta ce, a halin yanzu ba a tuhumar Janar Karenzi Karake kan zargin aikata laifukan yaki, ana zargin sa ne, a kan ayyukan ta’addanci.

Tuni dai ministan harakokin wajen kasar ta Rwanda Uwargida Louise Mushikiwabo ta rubuta rashin amincewar kasarta da kamun, a shafinta na twitter.

A nasa bangaren ministan shara’ar kasar ta Rwanda Busingye Johnston ya soke wata ziyarar aiki da yayi niyar kaiwa a kasar Spain, inda ya yi niyar ganawa da takwaransa Rafael Catala, kamar yadda majiyar hukumomin Spain ta sanar.

Tun shekara ta 2008 kotun kasar Spain ke bincike kan aikata laifukan yaki, da na kisan kare dangi, tare da ta’addanci da aka aikata a Rwanda, inda a karkashin haka ta bada sammacin kama mata manyan jami’an gwamnatin Rwanda 40 da suka hada da Janar Emmanuel Karenzi Karake.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.