Isa ga babban shafi
Ebola-Saliyo

Ebola na sake yaduwa a Saliyo

Mahukunta a kasar Saliyo sun tabbatar da sake dawowar Ebola a Freetown, babban birnin kasar, bayan mutum uku sun harbu da cutar a jiya Talata.

Jami'an kiwon lafiya da ke dawainiya da masu cutar Ebola
Jami'an kiwon lafiya da ke dawainiya da masu cutar Ebola REUTERS/Misha Hussain
Talla

Cibiyar da ke yaki da cutar Ebola a kasar ta ce lamarin na da matukar daga hankali kasancewar da anyi tsammanin an kammala shawo kan cutar a kasar, lura da cewa an shafe makonni ba tare da samun wanda ya kamu da cutar ba.

Cibiyar ta ce baya ga wadanan 3, akwai wasu 6 da a yanzu haka ake killace da su.

Ana dai fargabar cewa watakila cutar ta sake bazuwa saboda ta bulla a unguwar marasa galihu mai cunkoson Jama'a, inda ake yawan samun barkewar cutar Kwalera da Malarai.

A cikin watan da ya gabata ne aka sanar da cewar makwabciyar kasar ta Liberia ta rabu da Ebola, duk da dai  masana na gani cewar in dai cutar ba ta kare a saliyo da Guinea ba, toh akwai sauran aiki a gaba.

Tun daga wannan lokaci kawo yanzu akalla mutane 25 aka rawaito sun sake kamuwa da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.