Yau uku ga watan yuli, shekaru biyu cur kenan da kifar da zababbiyar gwamnatin dimokuradiyya ta Mohammad Morsi a kasar Masar.To sai dai a sakon da ta fitar a jajibirin wannan rana, jam’iyyar ‘yan uwa musulmi ta tsohon shugaba Morsi, ta yi kira ga magoya bayanta da su kaddamar da gagarumin bore domin kawo karshen abin da ta kira mulkin danniya da ake yi a kasar.A game da wannan hali da kasar ta Masar ta fada, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Malam Yakubu Yahaya Katsina na kungiyar ‘yan uwa musulmi a Najeriya, ga kuma yadda zantawarsu ta kasance.
Sauran kashi-kashi
-
Farfesa Umar Pate: Kan Ranar 'Yancin 'Yan Jarida ta Duniya
Yau ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar ‘yan jaridu ta duniya, inda ake nazari a kan kalubalen da ma’aikatan jarida ke fuskanta da kuma lalubo hanyoyin inganta aikin.03/05/202403:41 -
Farfesa Kelani kan zargin da NNPCL ta yi wa wasu dillalan mai a Najeriya
Kamfanin man NNPCL ya ce yana da wadataccen man da za'a kwashe sama da wata guda ana amfani da shi a cikin gida, yayin da ya zargi wasu gurɓatattun dilallai da jefa jama'ar ƙasar cikin halin ƙunci.02/05/202403:06 -
Nuhu Abayo Toro: Kan Ranar Ma'aikata ta Duniya
Yau ce ranar Ma’aikata ta Duniya, kuma bikin na wannan shekara na zuwa ne a cikin mawuyacin hali ga ma’aikatan Najeriya, sakamakon koma bayan tattalin arzikin kasar da kuma kuncin rayuwar da suka samu Kansu.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Nuhu Abbayo Toro, Sakatare Janar na kungiyar kwadago ta kasa ta TUC.01/05/202403:23 -
Dr. Kasim Kurfi: Kan rashin tsayuwar karfin naira
Bayan yin bazata wajen farfaɗowa daga faɗuwar da yayi a watannin baya, kuɗin Najeriya ya fuskanci koma baya musamman a makon jiya, inda a kasuwar canjin bayan fage aka sayar da dala guda kan Naira 1,400.01/05/202402:59 -
Tattaunawa da Bashir Ɗan Malam kan tsadar farashin mai a arewacin Najeriya
Harkokin kasuwanci da dama sun durkushe musamman a yankin arewacin Najeriya sakamakon tsadar farashin man fetur, inda ake sayar da lita guda a kan naira 2,000 zuwa 2,500 a kasuwar bayan-fage a jihar Sokoto. Kodayake akwai sassaucin farashin man a yankin kudancin kasar.29/04/202403:27