Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Sudan ta kudu ta cika shekaru 4 ba ci gaba

Sudan ta Kudu ta cika shekara hudu da samun ‘Yancin kai bayan ta balle daga Sudan a rana irin ta yau 9 ga watan Yuli, wannan kuma na zuwa ne bayan an shafe tsawon watanni 18 ana gwabza fada a jaririyar kasar.

Sudan ta Kudu ta cika shekaru hudu da samun 'Yancin kai bayan ta balle daga Sudan a ranar 9 ga watan Yuli
Sudan ta Kudu ta cika shekaru hudu da samun 'Yancin kai bayan ta balle daga Sudan a ranar 9 ga watan Yuli REUTERS
Talla

Sudan ta kudu ta fada cikin rikici ne a watan Disemban 2013, bayan shugaban kasar Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Riek Machar da yunkurin kifar da gwamnatinsa.

Rikicin kuma ya rikide ya koma na kabilanci tsakanin ‘Yan kabilar Dinka bangaren Salva Kiir da kuma kabilar Nuer bangaren Riek Machar.

Dubban mutane aka ruwaito sun mutu a rikicin na Sudan ta kudu, yayin da daruruwa suka fice daga kasar.

Majalisar Dinkin Duniya tace rikicin ya jefa al’ummar kasar cikin halin yunwa da karancin abinci, tare da bayyana cewa adadin mutanen kasar Miliyan 12 ke bukatar taimakon abinci.

Adadin mutanen Sudan ta kudu 616,000 aka kiyasta cewa sun tsallaka zuwa kasashen da ke makwabtaka da kasar da suka hada da Habasha da Uganda da Sudan da kuma Kenya

Har yanzu kuma babu wani alamu da ke tabbatar da za a kawo karshen rikicin kasar inda bangarorin da ke rikici suka yi watsi da yarjejeniyar tsagaita wuta da suka dade suna amincewa sau bakwai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.