Al Shebab za ta fadada hare harenta a gabashin Afrika
Shugaban Mayakan Al Shebab na Somalia ya yi barazanar kaddamar hare hare a kasashen gabashin Afrika a cikin wani sakonsa na Sallah da ya aiko a shafin Intanet a yau Juma’a.
Wallafawa ranar:
Kwamandan mayakan na Al Shabaab da ake kira Ahmed Umar Abu Ubaidah, ya ambaci kasashen gabashin Afrika da suka hada da Kenya da Habasha da Djibouti da kuma Uganda.
A cikin sakon, shugaban kungiyar ya ce ba zasu dai na kai hare hare a Kenya ba musamman saboda ‘yan uwansu da kasar ke yi wa mulkin mallaka.
Ya kuma yaba da mummunan harin da aka kai a Jami’ar garin Garissa a yankin arewa maso gabashin Kenya inda mayakan Shabaab suka bindige mutane 148.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu