Isa ga babban shafi
Somalia

An kashe mayakan al-Shebab da dama a Somalia

Mayakan kungiyar Al-shebab da dama ne aka kashe a cikin wani harin jiragen sama da na makaman atilare da aka kai masu a yankin kudancin kasar Somalia, kamar yadda mahukuntan kasar kenya da ke fama da hare-haren 'yan kungiyar suka sanar.

Mayakan al-Shebab dake Somalia
Mayakan al-Shebab dake Somalia AFP / M. Dahir
Talla

Ofisoshin Ministocin kasar Kenya 2 ne suka sanar da hare-haren da a cikinsu suka bayyana mutuwar 'yan kungiyar ta Al-shebab da dama.

Ofishin ministan cikin gidan kasar ya ce 'yan tawayen 30 suka mutu a yayin da ma’aikatar tsaron kasar ta Kenya ta ce dakarun rundunar kasashen Afrika a somalia  sun kashe 'yan al-shebab 50.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.