Isa ga babban shafi
Kenya-Somaliya

An bude ginin shagunan Westgate na Kasar Kenya bayan kisan mutane 67

A Kasar Kenya, yau ne aka sake bude ginin shagunan Westgate dake Nairobi babban birnin kasar domin ci gaba da gudanar da harkokrin kasuwanci. 

Ma'aikata a cikin ginin Shagunan na Westgate
Ma'aikata a cikin ginin Shagunan na Westgate REUTERS/Noor Khamis
Talla

Kusan Shekaru biyu kenan da ‘yan mayakan Al-Shebab dake Somaliya suka kaddamar da wani mummnunan hari tare da kashe mutane 67 a ginin shagunan, daya hada da masu siyayya da ma’aikata.

A lokacin harin dai, sai da aka shafe tsawon kwanaki hudu ana dauki ba dadi da mayakan na Al-shebab dake da alaka da kungiyar Al-Qaeda.

An kwashe watanni ana gyran ginin saboda barnar da mayakan suka yi wa ginin tare da kashe dalar Amurka akalla miliyan 20 wajen gyaran.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.