Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Zimbabwe ta dage dokar haramta Farauta

Hukumomin Kasar Zimbabwe sun cire dokar hana farauta da suka kafa bayan wani Ba’amurke ya kashe Zaki a kasar da ya haifar da cece kuce a duniya baki daya.

Zimbabwe ta dauki mataki akan Mafarauta bayan kisan Zaki
Zimbabwe ta dauki mataki akan Mafarauta bayan kisan Zaki REUTERS/A.J. Loveridge
Talla

Hukumar kula da gandun dajin kasar tace daga jiya litinin an cire haramcin farautar, saboda haka mafarauta na iya kutsa kai cikin dajin kasar.

Hukumar ta kuma ce jami’anta za su dinga raka mafarautan domin bada izini kafin farautar Zaki da Damisa da Giwa.

A cikin wata sanarwa, mahukutan Zimbabwe sun ce dole sai mutum ya samu izini kafin farautar Zaki da Giwa da Damisa.

Kuma duk wanda ya shiga farauta ba tare da izini ba zai fuskanci hukunci mai tsauri na haramta ma shi shiga farautar har abada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.