Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Ina nan a raye ban mutu ba inji Shekau

Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya musanta cewar an kashe shi, kuma ya ce har yanzu shi ke shugabancin kungiyar a wani sakon sauti da ya fitar a ranar lahadi.

Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau As received by Reuters
Talla

A fai-fan bidiyon da ya fitar da hausa, Abubakar Shekau ya yi watsi da kalaman shugaban kasar Chadi Idris Deby cewar an maye gurbin sa a shugabancin kungiyar, inda ya bayyana Deby a matsayin makaryaci kuma mai mulkin kama karya.

Shekau ya ce kafofin yada labaran marasa imani duk sun dauki labarin cewar an kashe shi, ko kuma bashi da lafiya, kuma bashi da karfin fada aji a cikin kungiyar, wanda ya ce hakan ba gaskiya bane.

Ya ce inda gaskiya ne da babu wanda zai ji muryar sa yanzu, saboda haka ya mika godiya ga Allah wanda ya ce da taimakon sa yana nan da ran sa, kuma ba zai mutu ba sai lokacin da Allah Ya diba masa ya cika.

A majon jiya ne shugaban kasar Chadi Idris Deby ya shaidawa Radio Faransa cewar an maye gurbin shugaban da Mahamat Dawud.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.