Isa ga babban shafi
Burkina

An hanawa ‘Yan Jam’iyyar Compaore shiga takara a Burkina

Kotun Tsarin mulki a kasar Burkina Faso ta yi watsi da takarar mutane 42 da suka fito daga jam’iyyar tsohon shugaban kasar Blaise Compaore a zaben kasar da za a gudanar a watan Oktoba.

Zéphirin Diabré, Dan takarar Shugaban kasa a Burkina Faso
Zéphirin Diabré, Dan takarar Shugaban kasa a Burkina Faso RFI/Yaya Boudani
Talla

Kotun ta fitar da jerin sunayen wadanda suka cancanci tsayawa takara a zaben shugancin kasar da kuma na ‘yan Majalisa da ake shirin gudanarwa a ranar 11 ga watan oktoba mai zuwa.

Kotun ta haramtawa wasu manyan shugabannin Jam’iyyar Compaore ta CDP shiga takarar zaben saboda zargin sun nuna goyon bayan ga shirin tsohon shugaban na yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima domin ba shi damar yin tazarce.

Sai dai kuma Jam’iyyar CDP a Burkina Faso ta yi kira ga magoya bayanta su fito zanga-zanga domin nuna adawa da matakin.

A ranar 31 ga watan Oktoban bara ne aka hambarar da gwamnatin Blaise Compaore wanda ya shafe shekaru 27 yana shugabanci a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.