Jam’iyyun adawa sun yi barazanar hana zabe a Cote D’Ivoire
Jam’iyyun adawa a kasar Cote D’Ivoire sun yi barazanar hana gudanar da zaben shugabancin kasar a ranar 25 ga watan okotba bai zuwa, matukar dai shugaba Alassane Ouattara ya ki zama da su domin warware wasu matsaloli kafin zaben.
Wallafawa ranar:
Jam’iyyun adawa 20 karkashin jagorancin tsohon firaministan kasar Charles Konan Banny, sun ce suna da shakku a game da batun tsaro da yakin neman zabe da kuma ita kan ta hukumar zaben kasar.
A jiya litinin aka fitar da jeren sunayen mutane 33 da ke neman takarar kujeran shugabancin kasar, wanda 3 daga cikinsu mata ne.
Kasar Cote d'voir ta fada cikin rikici da rashin zaman lafiya a shekarar 2010 bayan kammala zaben da tsohon shugaban kasar Laurent Gbabgo ya ki mika ragamar Mulkin kasar bayan ya sha kaye.
A cikin watan Afrilu Shekarar 2011 dakarun da ke biyaya ga Ouattara wanda ya yi nasara a zaben da taimakon Majalisar dinkin duniya da kasar Faransa suka tube Gbabgo daga Mulki.
Ouattara dai ya yi alkawarin gudanar da sahihin zabe a cikin kwanciyar hankali.
Sai dai ko a watan Yuni da ya gabata Dubun-dubatan Al'ummar kasar ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Abidjan kan nuna rashin jindadin su da mulkin Alassane Ouattara da suka ce bai tabuka abin a zo a gani ba a kasar da yaki ya tagayara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu