An Kashe sojojin Jamhuriyar Congo a Kivu
Wasu ‘Yan bindiga da ake zargin ‘Yan Tawayen Hutu ne sun harbe sojojin Jamhuriyar Demokradiyar Congo guda 6 har lahira a wani harin da suka kai kan iyakar kasar da ke Arewacin Kivu.
Wallafawa ranar:
Justin Mukanya, shugaban mulkin Yankin, yace an yiwa sojojin kwantar bauna ne a cikin motar su inda aka hallaka su.
Yankin Rutshuru na daga cikin yankunan da yan tawayen ke aika-aika.
Wani ma'aikacin leken asirin kasar da ke Goma wanda ya tabbatar da harin ya ce maharan sun yi amfani da rokoki wajen farwa dakarun a yankin kasar da ke iyaka da Uganda da Rwanda.
Shugaban kasar Joseph Kabila na fuskantar matsin lamba kasashen duniya wajen kawo karshan rashin zaman lafiya a kasar da kuma mukushe 'yan bindiga FDLR da ke haifar da rashin zaman lafiya a arewacin da kudancin Kivu, wanda ya tilastawa mutane da dama tserewa muhallinsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu