Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

‘Yan majalisar Afrika ta kudu sun yi watsi da matakin tsige Zuma

Wakilan majalisar Dokokin kasar Africa ta kudu sun sa kafa sun shure wani batu da aka gabatar na neman tsige Shugaban kasar saboda hannu wajen sulalewar Shugaban kasar Sudan Omar Hassan Al bashir da kotun ICC ke nema.

Shugaban kasar Africa ta Kudu, Jacob Zuma.
Shugaban kasar Africa ta Kudu, Jacob Zuma. REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Al Bashir wanda Kotun ke zargi da hannu wajen kashe rayukan dimbin mutane a yankin Darfur ya halarci kasar Africa ta kudu a watan shida da ya gabata, kuma an zaci za a yi masa kafar rago amma kuma ya samu ya sulale.

Shugaban Jamiyyar adawa a kasar Afrika ta kudun Mmusi Maimane da ya gabatar da bukatar tsige shugaba Jacob Zuma ya nemi majalisa ta binciki sakacin shugaban kasar da ya bari Al bashir ya bar kasar ba a kama shi ba.

Afrika ta kudu dai na da ‘yancin cafke Al Bashir saboda tana cikin mambobin kasashen da suka sanya hannu a kotun ICC da ke hukunta laifukan yaki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.