Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Zuma ya kare matakin rashin kame al Bashir

A Karo na farko shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, ya fito fili inda ya kare matakinsa na kin kama shugaban kasar Sudan Umar Albashir lokacin da ya ziyarci kasar a cikin watan Yunin da ya gabata, wanda Kotun ICC ke tuhuma da aikata laifukan yaki a yankin Darfur

Shugaban Sudan Omar Hassan Al Bashir
Shugaban Sudan Omar Hassan Al Bashir REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Shugaba Zuma wanda ke mayar da matarni a game da zargin da ‘yan adawa a majalisar dokokin kasar ke yi masa dangane da yadda ya bari Al Bashir ya sulale daga kasar a lokacin taron koli na kungiyar Tarayyar Afirka, ya ce shugaban na Sudan na da cikakkiyar kariya, domin kasancewar bakon kungiyar Tarayyar Afirka.

Jacob Zuma yace, Al Bashir ya shigo Afirka ta kudu ne ba wai bisa gayyatar kasar ba, sai dai a matsayinsa na bakon kungiyar AU, kuma kamar sauran shugabannin kasashen dole ne a ba shi kariya a tsawon lokacin da ya ke a cikin kasar.

Jagoran ‘yan adawa a Afirka ta kudu Mmusi Maimane, ya ce a matsayin Umar Hasan Al Bashir wanda kotun kasa da kasa ke nema domin hukuntar da shi dangane da zargin aikata kisan kiyashi da sauran laifufukan yaki, bai kamata a ce ya shigo sannan ya fice daga Afirka ta kudu ba tare da an cafke shi ba.

Sai dai daya daga cikin manyan masu adawa da Zuma Julius Malema, ya ce ba za su goyi bayan kasar ta kama wani shugaba na Afirka domin mika shi a hannun kotun duniya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.