Isa ga babban shafi
Rwanda-Amurka

Amurka taki amincewa da yunkurin shugaba Kagame na zarcewa a mulkin Rwanda

Amurka ta sa kafa tayi fatali da take taken da ake gani shugaban kasar Rwandan Paul Kagame nayi, na kokarin sauya kundin tsarin mulkin kasar, don neman ta zarce karo na 3 a kan karagar mulkin kasar.

shugaban Kasar Rwanda, Paul Kagame
shugaban Kasar Rwanda, Paul Kagame AFP PHOTO / FABRICE COFFRINI
Talla

Wannan na zuwa ne bayan da majalisar dokokin kasar ta Rwanda ta sauya kundin tsarin mulkin kasar, don baiwa shugaban damar yin takara.
Kagame, mai shekaru 57 a duniya na rike da madafun ikon kasar Rwandan tun cikin shekarar 1994, lokacin da kawo karshen kisan kare dangin da ‘yan kabilar Hutu masu tsatstsauran ra’ayi suka hallaka ‘yan kasar kusan Miliyon guda, akasarinsu ‘yan kabilar Tutsis.
Kasashen yammacin duniya sun bayyana goyon bayansu ga shugaban a wancan lokacin, sai dai kuma yanzu sun fara dawo wa daga rakiyarsa, sakamakom yadda suke masa kallon dan kama karya, daya rufe bakunan ‘yan adawan kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.