Wani Sojan Rwanda da ke Kasar Janhuriyar Tsakiyar Africa ya Kashe abokan aikin sa biyar
Wani sojan kasar Rwanda dake cikin ayarin dake wanzar da zaman lafiya a kasar Janhuriyar Tsakiyar Africa ya bude wuta kan abokan aikin nasa inda nan take ya kasha soja hudu kafin daga bisani ya kashe kansa.
Wallafawa ranar:
Akwai kuma wasu sojan takwas da ya jikkata, kafi ya kashe kansa.
Bayanai na nuna kafin wayewar gari Asabar lamarin ya auku.
Mai magana da yawun sojan wanzar da zaman lafiya a Bangui, Manjo-Janar Joseph Nzabamwita ya bayyana cewa suna binciken wannan alamari kafin su dauki matakin daya dace.
Dakarun dake wanzar da zaman lafiya a kasar Janhuriyar Africa ta Tsakiya sun kai 10,800 da suka fito daga kasashen Burundi, Cameroon, Congo,Janhuriyar Democradiyya ta Congo , Equitorial Guinea, Gabon, Rwanda, Morocco, Senegal, Pakistan da Indonesia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu