Isa ga babban shafi
Rwanda

'Yan majalisun Rwanda sun jefa Kuri'ar amincewa Kagame sake tsayawa takara

A yau talata ‘Yan majalisun Rwanda sun jefa Kuri'ar amincewa da batun canza kudin tsarin mulkin kasar, wanda zai baiwa Shugaban kasar mai ci Paul Kagame daman sake tsayawa takara a wani wa’adi na uku a jere.

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame .
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame . REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Rahotannin sun ce bangarori da dama, sun nuna amincewar su kan batun canza kudin tsarin mulkin kasar, wanda a baya bai amincewa Shugaba  ja ragamar mulkin kasar sama da sau biyu.

A cewar jaridun kasar amincewar  'yan majalisun  Datawa da na wakilan kasar ya biyo bayan bukatar wasu al’ummar na sake tsayawa takarar kagame a wa'adi na uku.

Paul Kagame mai shekaru 57 a duniya an zabe shi ne a matsayin shugaban kasar cikin shekarar 2003 inda ya samun rinjaye kuri’u da kaso 95, kana aka sake zaben sa a shekara ta 2010.

Kagame wanda kafin zaman sa Shugaba ya taka rawar gani wajen ceto kasar daga kazamin rikicin da ta tsinci kanta na 'yan tawayen Hutu, wanda ya yi sanadi mutuwar mutane da dama, ya ce bai tilastawa kowa ba kan batun canza kudin tsarin mulkin kasar ba, don haka zabi na hannu ‘yan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.