Isa ga babban shafi
Burkina

Sojoji sun yi juyin mulki a Burkina Faso

A yayin da ya rage 'yan makwanni a gudanar da zabe, Sojojin Burkina Faso sun tabbatar da yin juyin mulki a Kasar bayan sun fitar da wata sanar da aka yada ta kafafen Talabijin da Rediyo a yau Alhamis.

Lokacin da wani Sojan RSP ke srushe gwamanatin Michel Kafamdo ta kafar talabijin.
Lokacin da wani Sojan RSP ke srushe gwamanatin Michel Kafamdo ta kafar talabijin. RTB
Talla

Wannan dai na zuwa ne kwana guda da Dogarawan Shugaban Kasar mai rikon kwarya Michel Kafamdo suka tsare shi da Minikstansa Isaac Zida a fadar shugaban Kasa.

Rahotanni sun bayyana cewa a yanzu haka a na ta jin karar harbe harben bindiga a babban birnin Ouagadougou yayin da kuma aka girke dakarun Soji a kan titunan birnin.

Kawo yanzu dai ba a san halin da Shugaba Kafamdo da Firai Ministansa ke ciki ba, ko suna nan a raye ko kuma Sojin sun kashe su?

A ranar laraba ne sojojin dake goyon bayan tsohon hambararran shugaban Kasar Blaise Campore suka tsare Michel Kafamdo da Isaac Zida bayan sun kutsa kai a dai dai lokacin da ake kan gudanar da taron Majalisar Ministocin Kasar.

A watan Oktoban bara ne wani bore ya yi sanadiyar kifar da gwamantin Blaise Campore bayan ya yi yunkurin yin gyaran fuskka ga kundin tsarin mulkin Kasar da zai bai bashi damar ci gaba da zama kan kujerar shugabancin Kasar da ya shafe shekaru 27 a kai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.