Shugaba Alpha Konde na kasar Guinee Conakry, ya lashe zaben shugabancin kasar
Shugaban kasar Guinne Alpha Condé ya samu rinjayen da ake bukata a zagayen farko na zaben shugabancin kasar na ranar lahadin da ta gabata, kamar yadda sakamakon wucin gadi da hukuma zaben kasar ta bayyar ya nunar.
Wallafawa ranar:
Tuni dai yan adawa suka sa kafa suka yi fatali da sakamakon, tare da lasar takobin yin fito na fito da shi, ta hanyar shara’a da kuma zanga zanga kan tituna
Masu lura da al’amurran siyasar kasar sun bayyan matukar damuwarsu, kan fargabar ballewar tashe tashen hankulla sakamakon ayyana daya daga cikin bangarorin biyu da ya lashe zaben.
Sakamakon wucin gadin da hukumar zaben kasar CENI ta bayar a jiya juma’a, ya tabbatar da nasara ga shugaban kasar mai barin gado Alpha Konde da yawan kuri’u miliyan 2,2 a zaben da ya samu halartar kimanin kashi 92 % na masu zaben miliyan 6 dake kan kundin zaben kasar
Sakamakon wucin gadin da hukumar zaben kasar ta bayar dai, ya fito ne daga kashi 66 % na wadanda suka halarci zaben, wanda hakan ke nufin shugaba Konde da lashe zaben shugabancin kasar tun daga zagayen farko
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu