Isa ga babban shafi
Guinea

‘Yan adawa sun yi watsi da sakamakon zaben Guinea

‘Yan adawa a kasar Guinea Conakry sun kira zanga-zanga domin nuna adawa da sakamakon zaben kasar da hukumar zabe ta bayyana shugaba Alpha Conde a matsayin wanda ya samu nasara a zaben da aka gudanar a ranar 11 ga watan Oktoba.

Zaben shugaban kasa a Guinea
Zaben shugaban kasa a Guinea RFI/Guillaume Thibault
Talla

A ranar Asabar ne hukumar zaben Guinea CENI, ta sanar da sunan Shugaban Conde a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar tun a zagayen farko da sama da kashi 57 cikin 100 na kuri’un da aka kada akan babban mai adawa da shi Cellou Dalein Diallo, wanda ya samu kashi 31.44.

Cellou Dalein Diallo, ya yi watsi da sakamakon zaben tare da yin kir aga magoya bayan shi su fito domin kaddamar da zanga-zanga.

Sai dai kuma rahotanni sun ce zuwa yau Litinin babu alamun wani tashin hankali a kan titunan Conakry babban birnin kasar.

Tawagar masu sa ido na kungiyar Tarayyar Turai sun soki yadda aka gudanar da zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.