Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire

An yi zaben shugaban kasa cikin kwanciyar hankali a Cote d’Ivoire

A wannan Lahadi Al’ummar kasar Cote d’Ivoiresun gudanar da zaben shugaban kasa, inda shugaba mai ci Alassane Ouattara ke neman wa’adin shugabanci na biyu.

Jerin masu kada kuri'a a unguwar Koumassi da ke Abidjan, 25 ga watan oktoban 2015.
Jerin masu kada kuri'a a unguwar Koumassi da ke Abidjan, 25 ga watan oktoban 2015. AFP PHOTO / SIA KAMBOU
Talla

Da misalin karfe bakwai na safe agogon kasar aka bude rumfunan zabe kuma mutanen kasar sama da miliyan 6 ne suka cancanci kada kuri’unsu.

Kasashen duniya na sa ido, domin ganin an gudanar da zaben da fadin sakamako cikin kwanciyar hankali ba tare da tashin hankali ba, sabanin zaben 2010 da ya jefa kasar cikin yakin basasa.

Kimanin mutane 3,000 suka mutu a rikicin kasar bayan tsohon shugaban kasa Laurent Gbagbo ya ki yadda da shan kaye a zaben.

Akwai dai 'yan takara 7 a zaben, to sai dai manazarta na ganin cewa za a fi fafatawa ne tsakanin Ouattara da tsohon Firamnistan kasar Pascal Affi N’Guessan wanda ke takara karkashin jam’iyyar tsohon shugaban kasa Laurent Gbagbo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.