Isa ga babban shafi
Cote D'Ivoire

Kotu ta fitar da sunayen 'Yan takarar shugabancin Ivory Coast

Kotun tsarin Mulkin Kasar Ivory Coast ta bayyana sunayen Mutanen da zasu tsaya takarar shugabancin Kasar, a zaben da za a gudanar a ranar 25 ga watan Oktoba mai zuwa, kuma sama da mutane miliyan 6 ne ake sa ran zasu kada kuri’u a wannan karan.

Shugaban Kasar Ivory Coast Alassane Ouattara
Shugaban Kasar Ivory Coast Alassane Ouattara REUTERS/Luc Gnago
Talla

A jumulce dai mutane 33 ne suka bukaci tsayawa takarar shugabancin Kasar, da ya hada da Pascal Affi N’Guessan, shugaban Jam’iyyar tsohon shugaban Kasar Laurent Gbagbo da kuma tsohon Firai Ministan Kasar Charles Konan Banny, harma da tsohon Kakakin Majalisar dokoki Mamadou Koulibaly.

To sai dai Kotun ta soke sunayen mutane 23, inda ta bar mutane 10 da zasu kalubalanci shugaba mai ci a yanzu Alassane Ouattara.

Za a fara gudanar yakin neman zabe a ranar 11 ga watan Oktoba mai zuwa kafin daga bisani a gudanar da zaben a ranar 25 a cikin watan, yayin da ake sa ran zaben na wannna karan zai taka rawar gani wajan maido da kwanciyar hankali a Kasar ta Ivory Coast wadda ta yi fama a rikici bayan zaben da ta gudanar a shekarar 2010, inda sama da mutane dubu 3 suka rasa rayukansu.

Shugaba Ouattara mai shekaru 73 a rayuwarsa zai sake neman wa’adi na biyu a kan karagar mulki bayan ya yi nasarar darewa kan kujerar shugabancin Kasar shekaru biyar da suka gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.