Isa ga babban shafi
Chadi

Sojojin Chadi sun kashe mayakan Boko Haram

Gwamantin Chadi ta bayyana cewa Sojojinta sun fatattaki mayakan Boko Haram tare da kashe 14 daga cikin su bayan sun kaddamar da hare hare kan Sojojin a kusa da tafkin Chadi.

Sojojin Chadi da ke yaki da Boko Haram.
Sojojin Chadi da ke yaki da Boko Haram. AFP PHOTO / MIGUEL MEDINA
Talla

Wata sanarwa da gwamantin kasar ta fitar ta ce, daya daga cikin mayakan na Boko Haram ya tarwatsa kansa tare da jikkata fararan hula 11 bayan ya tayar da bam din da ya ke dauke da shi a jikinsa.

A ranar 10 ga watan jiya ne wasu jerin hare hare uku suka kashe mutane 41 a Baga Sola da ke kusa da tafkin na Chadi, inda dubban ‘Yan Najeriya da Chadi ke samun mafaka bayan sun kauracewa gidajensu saboda rikicin Boko Haram.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.