Isa ga babban shafi
Fadar Vatican

Fafaroma ya damu da rikicin Afrika ta tsakiya

Shugaban Mabiya darikar Katolika a duniya Fafaroma Francis ya bayyana damuwarsa kan sabon tashin hankalin da aka samu a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, makwanni hudu kafin ya kai ziyara a kasar.

Shugaban darikar katolika ta duniya Fafaroma Francis.
Shugaban darikar katolika ta duniya Fafaroma Francis. REUTERS/Jim Bourg
Talla

Yayin da ya ke jawabi ga masu ziyarar ibada a dandalin St Petersburg Vatican, FaFaroman ya ce sabon tashin hankalin ya dada jefa al’ummar kasar cikin halin kun ci.

Rahotanni sun ce an samu barkewar tashin hankali tsakanin bangarorin da ba-sa-ga maciji da juna a Bangui, abinda ya yi sanadiyar kashe mutane biyu da kuma raunana wasu da dama.

Afrika ta tsakiya ta fada cikin rikici ne a 2013 bayan ‘Yan tawayen Seleka yawancinsu Musulmi sun hambarar da gwamnatin Francois Bozize. Daga lokacin ne kuma rikicin kasar ya rikide ya koma na addini tsakanin Seleka da anti-balaka Kiristoci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.