Isa ga babban shafi
Saliyo

An kawar da cutar Ebola a Sierra Leone

Hukumomin kiwon lafiya a kasar Saliyo sun ce an kawo karshen cutat Ebola a kasar, bayan da aka share tsawon kwanaki 42 ba tare da an samu wani da ya kamu da ita ba a duk fafin kasar.

Jami'an yaki da annaboar Ebola a birnin Freetown na Sierra Leone
Jami'an yaki da annaboar Ebola a birnin Freetown na Sierra Leone © Reuters
Talla

A wannan asabar shugaban kasar Bai Koruma na jagoranci wani gagarumin biki domin murnar kawo karshen annobar, wadda a cikin shekaru biyu ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu hudu a kasar.

Bayan kawo karshen cutar a Sierra Leone, a yanzu dai hankula sun karkata ne zuwa ga kasar Guinee Conakry wadda ita ma ke fama da cutar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.