Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 8 sun mutu a harin Maiduguri

Akalla mutane 8 aka tabbatar da mutuwarsu a harin kunar bakin wake da wata mata ta kai a ranar Lahadi a sansanin ‘yan gudun hijira a Maiduguri Jihar Borno.

Mayakan Boko Haram sun jima suna kai hare hare a Maiduguri
Mayakan Boko Haram sun jima suna kai hare hare a Maiduguri AFP PHOTO
Talla

Wadanda suka mutu sun hada da Mata da kananan yara da suka fito daga Dikwa saboda rikicin Boko Haram zuwa garin Maiduguri.

Wani dan kato da gora da ke kula da sansanin ‘Yan gudun hijirar ya shaidawa RFI Hausa cewa matar ta tayar da bom din ne a lokacin da suke tantance mutane a kofar shiga sansanin ‘Yan gudun hijira.

A cewar shi suna cikin tantance Mata ne ‘Yar kunar bakin waken ta zame ta tayar da bom din da ke jikinta.

Akalla mutane 8 suka mutu, bakwai kuma suka jikkata sakamakon harin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.