Isa ga babban shafi
Najeriya-Amnesty

Amnesty na son a gurfanar da yan Boko Haram

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bukaci hukumomi a tarayyar Najeriya da su yi iya kokarinsu domin tabbatar da cewa an gurfanar da magoya bayan kungiyar Boko Haram da kuma wadanda ke taimaka wa kungiyar domin kashe jama’a.

Wasu daga cikin mayyakan kungiyar Boko Haram
Wasu daga cikin mayyakan kungiyar Boko Haram AFP PHOTO / STRINGER
Talla

Shugaban sashen bincike na kungiyar a yankin Afrika Netsanet Belay, ya bayyana a wata sanarwa cewa, lura da irin tu’anniti da kuma kisan jama’a bila adadin, ya kamata hukumomi su yi dukannin abinda ya wajaba domin hukunta magoya bayan kungiyar.

To sai dai Amnesty International ta ce alhaki ya rataya a wuyan gwmanati da ta kara daukar matakai domin kare al’umma da kuma dawo da doka musamman a yanki arewa maso gabashin kasar
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.