Sama da mutane miliyan 50 na cikin barazanar fuskantar yunwa Afrika - Rahoto
Wani bincike da gwamman hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya suka yi a ƙasashe 17 ya nuna cewa sama da mutane miliyan 50 ne za su fuskanci matsalar ciyar da kansu a yankunan yammaci da tsakiyar nahiyar Afrika a kaka mai zuwa.
Wallafawa ranar:
Binciken da aka yi da haɗin gwiwar gwamnatoci da ƙungiyar ƙasashen yammacin nahiyar Afrika ta ECOWAS, an yi shi ne a ƙasashen da suka haɗa da Senegal da Burkina Faso da Mali da Jamhuriya Nijar da Kamaru da kuma Najeriya.
A wannan yanki mai girma, rahoton binciken ya ce mutane miliyan 52 ne za su fuskanci matsala wajen ciyar da kansu da kaka mai zuwa, wato a yayin girbi kenan, tsakanin watan Yuni zuwa Agusta, abin da ke nuni da cewa an samu ƙarin mutane miliyan 4 da za su shiga wa wannan hali idan aka kwatanta da na bara.
Rahoton ya yi ƙarin bayanin cewa, kashi 12 na wannan adadin, ko kuma mutum ciki kowane 10 zai fuskanci matsala wajen samun nau’in abinci mai gina jiki a yankunan yammaci da tsakiyar Afrika a wannan lokaci, duba da hasashen da gwamman kungiyoyi, ciki har da Oxfam da Unicef suka yi.
Idan aka ware ƙasashen Guinea, Jamhuriyar Benin, Ghana da Ivory Coast, ana sa ran ta’azzarar matsalar ƙarancin abinci a dukkannin ƙasashe 17 da aka gudanar da wannan bincike.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu