Isa ga babban shafi
Vatican

Fafaroma ya nufi Afrika ta tsakiya daga Uganda

A yau Lahadi Shugaban Darikar katolikta Fafaroma Francis zai nufi kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya mai fama da rikici bayan ya kammala ziyara a kasar Uganda inda ya samu kyakkyawar tarba a jiya Assabar.

Shugaban mabiya darikar Katolika Fafaroma Francis ya samu kyakkyawar tarba a Uganda
Shugaban mabiya darikar Katolika Fafaroma Francis ya samu kyakkyawar tarba a Uganda REUTERS/Giuseppe
Talla

Dubban kiritoci ne ake sa ran zasu hada gangami domin tarbarsa a Bangui babban birnin kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da ta shafe shekaru sama da biyu cikin rikici mai nasaba da addini.

Ana sa ran a cikin jawabin da zai gabatar, Fafaroman ya jawo hankalin al’ummar kasar game da zaman lafiya da juna tsakanin addinai.

Faransa da ke taka muhimmayar rawa ga aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya, ta yi gargadi akan ziyarar da Fafaroma zai kai a kasar, saboda barazanar tsaro.

Sama da shekaru 2 ke nan dai da Afrika ta tsakiya ke fama da rikici mai nasaba da addini kuma shugabar rikon kwaryar kasar Uwargida Catherine Samba Panza ta ce tana son Fafaroma ya zo kasar, domin isar da ishara da zai taimaka a kawo karshen rikici a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.