Isa ga babban shafi
CONGO

Mutane 22 sun bata a tafkin Kivu

Mutane sama da 22 suka bata lokacin da wani kwale-kwalen da suke ciki ya kife a tafkin Kivu da ke gabashin Janhuriyar Demokiradiyar Congo. Gwamnan Arewacin Kivu Julien Paluku ya ce kwale-kwalen ya kife ne da mutane 47 inda aka yi nasarar ceto 22 daga cikinsu.

Tafkin Kivu  a jamhuriyyar Congo
Tafkin Kivu a jamhuriyyar Congo Photo MONUSCO/Abel Kavanagh
Talla

Lamarin dai ya faru ne a ranar Litinin kuma Akwai yaro dan shekaru 5 da aka tabbatar da ya mutu.

Gwamnan yace kwale kwalen ya taso ne daga Kivu zuwa Bukavu lokacin da aka samu hatsarin.

Hatsarin jiragen ruwa ba sabon abu ba ne a ruwan Congo, inda mutane suka dogara da kwale-kwale ga harakar sufuri.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.