Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

Ana fama da kwalera a Congo

Cutar Kwalera ko Amai da Gudawa ta yi sanadiyar mutuwar mutane 35 a Jamhuriyar Demokradiyar Congo a yayin da wasu 1,500 ke fama da cutar kamar yadda rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a jiya Laraba ya bayyana.

REUTERS/Andreea Campeanu
Talla

An sami barkewar cutar ne a yankunan kudancin kasar goma sha biyar inda aka tabbatar da mutane 1520 suka kamu da cutar yayin da 35 daga cikinsu suka rasa rayukansu.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana matukar damuwarta game da cutar amai da gudawa da ke addabar wasu yankunan kasar.

Majalisar ta yi kira ga jama'a da su dauki matakan kula da kiwon lafiya domin kare kansu daga kamuwa da cutar.

Wani mai magana da yawun hukumar aikin jin kai a Jamhuriyar Congo Sylvester Ntumba ya ce kasar na fama da rashin samar da tsaftataccen ruwan sha da kuma wasu matakai na tabbatar da tsaftar muhalli abin da ke kara barazanar ga rayuwar al’umma kasar .

Ya ce yankin garin Katanga inda aka samu bullar cutar matsalar ruwan sha da kuma wuraren ba-haya na daya daga cikin bukatun al’ummar yankin.

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce idan ba a yi kokarin shawo kan matsalar ba akwai yiyuwar yaduwar cutar zuwa wasu sassan kasar

A tsakanin shekara ta 2012 zuwa 2014 sama da mutane 9,000 ne suka rasa rayukansu sakamkon annobar cutar amai da gudawa a Jamhuriyar Demokradiyar Congo.

A shekarun baya ma mutane sama da dubu bakwai ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar amai da gudawa a Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.