Isa ga babban shafi

Mahamat Idriss Deby ya lashe zaɓen Chadi da gagarumin rinjaye

Sakamakon zaɓen shugaban kasa a Chadi ya bayyana jagoran mulkin Sojin Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin wanda ya lashe zagayen farko na zaɓen wanda ke nuna yiwuwar ya iya tsawaita wa’adin mulkin iyalan gidan Deby na wasu karin shekaru.

Zababben shugaban kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby.
Zababben shugaban kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby. REUTERS - Stringer
Talla

Zaɓen na ranar Litinin ya kawo karshen mulkin riƙon ƙwarya na shekaru 3 da Chadi ta fuskanta tun bayan mutuwar shugaba Idris Deby Itno a fagen daga wanda ya baiwa ɗansa Janar Mahamat Deby damar jan ragamar kasar mai fama da rikice-rikice baya ga ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Sakamakon zaɓen da hukumar zaɓe ta ANGE ta fitar ya nuna yadda Mahamat Deby da aka fi sani da Kaka ya lashe jumullar kashi 61.3 na yawan ƙuri’un da aka kaɗa yayinda Firaministan ƙasar Success Masra ya lashe kashi 18.53.

Kowanne lokaci daga yanzu ne ake dakon kotun kundin tsarin mulki ta tabbatar da sahihancin zaɓen.

Sai dai tuni Firaminista Masra ya ƙalubalanci sakamakon wanda ya bayyana da marar inganci.

A bangare guda tuni Shugaba Mahamat Deby Itno ya gabatar da jawabin kai tsaye ta gidan talabijin tare da godewa al’ummar ƙasar kan zaɓensa baya ga shan alwashin samar da yanayi mai inganci ga al’umma.

Tun gabanin sanar da sakamakon zaɓen anga yadda dubunnan magoya bayan Deby suka  fara murnar samun nasara a kan titunan birnin N’Djamena fadar gwamnatin Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.