Bangarorin Libya sun amince su sasanta
Bangarorin da ke rikici a Libya sun ce sun cim ma yarjejeniya a tattaunawar sulhu da suke gudanarwa a Tunisia domin kawo karshen tashin hankalin da kasar ta shiga tun kawar da gwamnatin Kanal Gaddafi.
Wallafawa ranar:
Tattaunawar ta kunshi bangaren gwamnatin da ke iko a Tripoli da kuma bangaren da ke shugabanci a gabashin kasar.
Bangarorin biyu sun amince a zabo wakilai tsakaninsu da zasu kafa kwamiti domin zaben sabon Firaminista nan da kwanaki 15, sannan za a samar da wani kwamiti da zai diba kundin tsarin mulki.
Sai dai kuma duk da wannan matakin, wasu na ganin sai bangarorin biyu sun yi maganin mayakan IS da suka samu wurin zama birnin Sirte.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu