Sabon rikici ya kuno kai a Sudan ta Kudu
A yau Talata sabon rikici ya barke a Sudan ta Kudu, bayan wasu ‘yan bindiga sun bude wuta a wani yanki da ke yammacin kasar, batun da a yanzu ya fara haifar da furgaba sake komawa kasar gidan jiya, na rashin zaman lafiya duk da yarjejeniyar zaman lafiya da ka cimma watanni baya.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce tuni mutane yankin suka fara tatara inasu, suna hijira domin tsira da ransu, al’amarin da ke zuwa a dai-dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke bayyana bukatarta na dawo da fararn hula kasar, wadanda ke hijira saboda rashin kwanciyar hankali a kasar.
Wasu kafafa yadda labaran kasar sun rawaito cewa fadan ya fara ne a yankin Yambio tsakanin Sojoji da kungiyoyi wasu matasa da ke dauke da makamai, wanda a baya aka rawaito cewa suna aiki tare ‘yan tawayen kasar da ke samun goyon bayan Riek Machar.
Rikicin da a yanzu ya fadada har zuwa yankuna kasar 3, ya sabawa sharuda yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin kasar ta cimma da 'yan tawayen a watan Augustan da ya gabata, na kawo karshan yakin kasar da aka kusan shafe shekaru 2 ana fama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu