Isa ga babban shafi
Rwanda

An cafke Ntaganzwa na Rwanda da ake nema ruwa a Jallo

Majalisar dinkin duniya ta sanar da cafke 1 daga cikin mutane 9 da ake nema ruwa a jallo, kuma tsohon Magajin gari a kasar Rwanda bisa zargin hannu a harin kisan kiyashi da ya hallaka duban mutane a shekarar 1994 a kasar.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Rwanda
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Rwanda AFP PHOTO / Pacome PABANDJI
Talla

Ladislas Ntaganzwa wanda Amurka ta sanya tukuici dala miliyan 5 ga duk wanda ya taimaka wajen cafke shi, za a tuhumi shi ne kan laifukan yaki da keta hakkin bil’adama.

Akalla mutane dubu 800 mafi yawa kabilar Tutsi aka kashe a yakin tsawon kwanaki 100 da aka yi a kasar da Hutus.

Mai shigar da kara a Rwanda Richard Muhumuza ya ce bayan laifukan Yaki ana zargi Ntaganzwa da aikata fyade da lalata da mata da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.