Isa ga babban shafi
Rwanda-Faransa

Rwanda ta ki gayyatar Faransa a bikin juyayin kisan kiyashi

A yau litinin ne ake bikin cika shekaru 20 da kisan kiyashin da aka yi a kasar Rwanda inda aka samu hasarar rayukan dubban mutane. Rwanda ta janye goron gayyatar da ta ba Faransa domin halartar bikin bayan shugaba Paul Kagame ya zargi kasar da hannu a kisan kiyashin da ya auku a shekarar 1994.

Ana juyayin kisan kiyashin da ya auku a kasar Rwanda
Ana juyayin kisan kiyashin da ya auku a kasar Rwanda REUTERS/Noor Khamis
Talla

Sa-in-sar da ke tsakanin Rwanda da Faransa shi ne ya karkatar da hankalin duniya daga bikin cika shekaru 20 na tuna kisan kiyashin da ya auku a Rwanda a 1994.

Jekadan Faransa Michel Flesch, da zai wakilci kasar a taron bikin, yace Gwamnatin Rwanda ta sanar da janye goron gayyatar a wata tattaunawa tsakanin shi da ma’aikatar harakokin wajen kasar ta wayar tarho.

Wannan kuma ya biyo bayan zargin da shugaban Rwanda Paul Kagame ya yi akan Faransa tana da hannu a kisan dubban ‘yan kabilar Tutsi.

Kuma a cikin kalaman Kagame da aka wallafa a mujallar Jeune Afrique, yace Faransa ta aika da dakarunta kafin a fara kisan kiyashi a kasar.

Faransa ta dade tana musanta zargin na Rwanda, tana mai jaddada cewa dakarunta sun je kasar ne domin kare fararen hula.

Wannan wata sabuwar baraka ce ta kunno kai a huldar kasashen biyu bayan sun sasanta a 2010.

Tuni kasar Belgium da ta yi wa Rwanda mulkin mallaka ta nemi afuwa saboda rashin samun nasarar hana aukuwar kisan kiyashin.

Za a kwashe tsawon kwanaki ana juyayin dubun dubatar mutanen da Sojin gwamnati da mayakan Hutu suka kashe a Rwanda.

A sakonsa Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon yace wannan darasi ne ga Syria da Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.