An kashe ‘Yan kunar bakin wake a Kamaru
Sojojin Kamaru da ‘Yan banga sun murkushe wani yunkurin kai hari da wasu ‘Yan mata biyu suka shirya kai wa a garin Kolafata da ke kan iyaka da Najeriya.
Wallafawa ranar:
Jami’an tsaron sun kashe ‘Yan matan ne da ke rataye da bama bamai a jikinsu a ranar Litinin.
‘Yan banga sun harbi yar kunar bakin guda da mashi, yayin da Sojoji suka dauke guda da bindiga kafin su tayar da bom din da ke jikinsu.
Rahotanni sun ce baya ga mutuwar ‘Yan kunar bakin waken babu wani da ya mutu ko ya ji rauni.
Ana zargin ‘Yan Boko Haram ne suka yi yunkurin kai harin wadanda ke ci gaba da addabar yankin arewacin Kamaru.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu