Isa ga babban shafi
Tafkin Chadi

Shugabannin Afrika sun nemi taimako kan ceto Tafkin Chadi

Shugabannin Kasashen Afirka sun bukaci takwarorinsu na duniya su taimaka wajen ceto tafkin Chadi wanda ke ci gaba da shanyewa sakamakon matsalar sauyin yanayi.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari na jawabi a taron sauyin yanayi a Paris
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari na jawabi a taron sauyin yanayi a Paris REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Shugabanin kasashen da ke kula da tafkin Chadi da suka hada da na kasashen Kamaru da Chadi da Nijar da Najeriya sun bukaci taimako don kare tafkin da kuma samar da tsaro ga mutanen da ke kewaye da shi.

Shugaban Nijar Muhamamdou Issoffou ya fadawa gangamin shugabannin kasashen duniya a taron sauyin yanayi a Paris cewa tafkin Chadi na daf da mutuwa, yayin da takwaransa na Chadi Idris Deby ya sahidawa shugabannin na duniya cewa ya zuwa yanzu tafkin ya tsotse matuka daga yadda fadinsa ya ke a shekarar 1960.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace janyewar tafkin ke haifar da mutanen yankin suna kwarara zuwa Turai, tare da neman karkata wani kogi don hana tafkin Chadi daga karewa.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kasashen duniya su taimaka wajen ceto tafkin da kuma samar da tsaro a Yankin. Tuni dai kasashen Birtaniya da Faransa da Amurka suke taimakawa Yankin don samar da tsaro.

Majalisar Dinkin Duniya tace kimanin mutane miliyan biyu da rabi suka rasa matsaguni a tafkin chadi saboda shanyewar tafkin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.