Hollande ya bukaci kasashen duniya su amince da yarjejeniyar sauyin yanayi
Shugaban Faransa Francois Hollande ya yi kira ga kasashen duniya su amince da yarejejeniyar Majalisar dinkin duniya a taron sauyin yanayi da za a fara a ranar Litinin a birnin Paris.
Wallafawa ranar:
Ko da ya ke, Shugaban na Faransa da ke jawabi a taron kasashen renon Ingila a Malta ya bayyana fargaba akan wasu kasashe da ya ce suna iya kawo cikas ga bukatun da ake son cim ma a taron, wanda zai kunshi shugabannin kasashe 150.
A taron dai shugabannin kasashen duniya zasu tattauna ne, tare da yin muhawara kan amincewa da wasu bukatu na rage gurbatar muhalli da ke haifar da canyin yanayi a duniya, musamman kasashe masu manyan masana’antu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu