Isa ga babban shafi
Yemen

Guguwa tafe da ruwa mai karfi ta ratsa Yemen

Wata guguwa tare da ruwan sama ta afka wa kasar Yemen , inda ta haifar da gagarumar ambaliyar ruwa tare da yin illa a yankin da kungiyar Al-Qaeda ta mamaye wanda kuma ke fama da tashe tashen hankula.

RFI/Christophe Paget
Talla

Ministan ma’aikatar kamun kifi ta kasar Fahd Kafain ya shaida wa kamafanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, suna fargabar samun asarar rayukan Jama’a lura da irin karfin guguwar.

Sama da mutane 200 dai suka samu raunuka, yayin da daruruwan gidaje suka rushe sakamakon karfin guguwar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.