Isa ga babban shafi
Mexico

Mahaukaciyar Iska da Ruwan Sama ta ratsa Mexico

Wata mahaukaciyar goguwa da ruwan sama na chan ta ratsa kasar Mexico, tana ta barna, da ture itatuwa da dukkan abinda ta ci karo dashi, amma kamar yadda majioyoyi ke cewa babu rasa rayuka ya zuwa yanzu. 

Mutane a Mexico na ta neman mafaka sakamakon  mahaukaciyar iska da ruwan sama
Mutane a Mexico na ta neman mafaka sakamakon mahaukaciyar iska da ruwan sama REUTERS/Henry Romero
Talla

Tun kafin wannan lokaci Hukumomin kasar sunyi ta tattara mutane zuwa tudun mun tsira.

Mahaukaciyar iska da goguwar da ruwan sama da aka sanya mata suna Hurricane Patricia, masana yanayi sun nuna tana da munin gaske kuma zata haifar da mummunan hasarar rayukan jama'a  da dukiya.

Masana sun ce mahaukaciyar iska da ruwan saman na tafiyar kilomita 325 cikin awa daya.

Shugaban kasar Enrique Pena Nieto ya roki mutan kasar da su yi hattara kuma a sami inda za'a fake har a sami saukin wannan masifa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.